Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Tattaunawa Kan Cin Zarafin Mata A Gidan Aure-Kashi Na Daya-Mayu 12, 2022


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Cin zarafin iyali na daya daga cikin batutuwa da muka sha yin Makala a kai lamarin da yake shafar iyaye maza da mata da kuma kananan yara. Sai dai bincike na nuni da cewa, matsalar ta fi shafar mata da kananan yara da sau da dama ya kan kai ga rasa rayuka.

Akasin tunani da ake yi cewa, lamarin yafi shafar marasa ilimi ko marasa galihu, alkaluma na nuni da cewa, lamarin yana shafar matan aure ‘yan Boko da dama, lamari na baya bayan nan shine fitacciyar mawakiyar nan Osinachi Nwachuku wadda ake zargin mijinta da gasa mata akuba na tsawon shekaru takwas daga karshe ya zama ajalinta.

A yau shirin ya sami bakuncin Ministar harkokin mata a Najeriya Pauline Tallen, da kuma Mustapha Suleiman shugaban wata kungiyar matasa da ake kira, “Youth Assembly Of Nigeria” domin nazarin wannan lamarin da nufin neman hanyar shawo kan matsalar.

Saurari kashin farko na tattaunawar da wakiliyar Sashen Hausa Medina Dauda ta jagoranta:

Tattaunawa Kan Cin Zarafin Mata A Gidan Aure-Kashi Na Daya:10:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:21 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG