A ci gaba da nazarin batun ba mata kashi talatin da biyar cikin dari na guraban siyasa a Najeriya da majalisar dokokin kasar ta yi fatali da shi, yau ma muna tare da Tsohuwar Ministar mata Aisha Isma’il da Barrista Hassana Ayuba Mairiga, da kuma ‘yar gwaggwarmaya Balaraba Abdullahi. A tattaunawar ta yau sun tabo batutuwa da suka hada da dalilan da suke gani ya sa 'yan majalisa su ka ki amincewa da kudurin.
Saurari tattaunawar da Madina Dauda ta jagoranta:
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.