Idan kuna biye da mu makon da ya gabata muka fara haska fitila kan tsaka mai wuya da iyaye suka shiga dangane da batun ilimin 'ya'yan su, wadanda ke fuskantar barazanar tsaro musamman a makarantun kwana.
Bakin da muka gayyata a shirin su ne Ibrahim Mohammad Sani, da Bashir Musa Ibrahim mukaddashin shugaban kungiyar kare hakkin bil’adama ta duniya reshen jihar Kano, da Aminu Mohammed mai wakiltar kungiyar dalibai da ke sa ido a ayyukan gwamnati.
Saurari ci gaban hirar da wakiliyarmu Baraka Bashir da ta jagotanta.
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.