Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI:Tattaunawa Kan Tarbiyar 'Ya'ya- Kashi Na Biyu -Maris 25, 2021


Alheri Grace Abdu

Idan kuna biye da mu makon da ya gabata shirin Domin Iyali ya sake haska fitila kan batun tarbiyar yara, wani abu da ya ke da muhimmanci ga yadda al'umma ke kallon iyali, da kuma yanke hukumci ko iyaye zasu amince su hada zumunci aure da wani iyali.

Bakin da muka gayyato domin tattaunawa kan wannan hatun sun hada da Musa Saleh Muktar, da Rabi Abdullahi, da Hannatu Baba Bello da kuma Maitadda Sabo Mohammed iyaye kuma 'yan gwaggwarmaya.

A yau, jagorar tattaunawar, Baraka Bashir ta fara da tambayar Mallam Musa Saleh Muktar, abinda ya sa wadansu maza su ke tsautawa mata da cewa, menene ya sa su ke takurawa yara bisa hujjar cewa ai gidansu ne.

Saurari bayyaninsa da kuma sauran batutuwan da aka tabao a tattaunawar:

DOMIN IYALI:Tattaunawa Kan Tarbiyar 'Ya'ya- Kashi Na Biyu-10:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:18 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG