Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Amsa Cewa Ya Yi Magana Da Shugaban Ukraine Kan Almundahana


Shugaban Amurka, Donald Trump, ya amsa cewa ya yi magana akan batun matsalar almundahana da shugaban kasar Ukraine, Volodymrs Zeleskiy, to amma bai zarce da cewa sun tattauna kan batun binciken dan takarar jam’iyyar Demokarat mafi fice, wato Joe Biden ba.

Jaridar Wall Street Journal ta ce har sau takwas Shugaba Trump ya bukaci Zeleskiy da ya binciki Biden da dansa Hunter, da kuma ko wani kamfanin Iskar Gas na Ukraine ya yi kokarin samun alfarma ne da ya dauki Hunter aiki a lokacin Joe Biden ya na Mataimakin Shugaban Amurka.

Rahotannin sun ce Trump ya na kokarin ya ga Zelenskiy ya hada kai da lauyan shi Trump din, Rudolph Guiliani, wajen abincikin Biden da dansa.
Trump ya kira Zelenskiy ne tun a watan Yuli, watanni biyu bayan da ya hau kan karagar mulki a Ukraine.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG