Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump ya zama sabon shugaban kasar Amurka


Sabon shugaban Amurka

An rantsar da Donald Trump a matsayin sabon shugaban Amurka na 45, inda ya gabatar da jawabi ga Amurkawa da duniya baki ‘daya.

Shugaban mai shekaru 70 da haihuwa ya zamanto shugaba nan a farko da yawan shekaru da ya taba zama shugaban Amurka a tarihi. Wanda ya ‘dauki alkawarin kare ‘kasarsa da muradunta.

Dubban mutane suna goyon bayan sabon shugabanne a dalilin kalamin da yayi lokacin yakin neman zabe ‘make America great again’ wato sake maido da martabar Amurka.

Taron bikin tsantsarwar ya cika makil da tsofaffin shugabannin Amurka da suka hada Jimmah Cater da George W. Bush da Bill Cliton da kuma shugaba mai barin gado Barack Obama.

'Yar takarar shugabancin Amurka da ta sha kaye a zaben shekara ta 2016 Hillary Clinton, itama ta halarci taron.

XS
SM
MD
LG