Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matar Shugaban Amurka Ta Farko Da Aka Haifa A Wata ‘Kasa


Donald Trump da matarsa Melania

Melania Trump, ta zamanto matar shugaban ‘kasar Amurka ta farko cikin shekaru kusan 200, a matsayin macen da aka haifa a wata ‘kasa ta daban ba Amurka ba.

Kafin Donald Trump ya kaddamar da kamfen din sa, yawancin mutane basu san komai game da Melania ba ko inda aka haife ta. Melania dai an haife ta ne a wata karamar ‘kasa mai suna Slovenia.

Matar Donald Trump ta farko da yanzu basa tare kuma suka sami 'ya'ya uku tsakaninsu ita ce Ivanka. Bayan mutuwar aurensu ya auri Mala Mapos wadda ya saketa bayan wani dan lokaci.

A shekarar 2005 Donald Trump ya auri matarsa ta yanzu Melania mai son kayan ado kuma tana nuni kayan adon.

Wadda a tarihin Amurka itace matar shugaban ‘kasa ta farko cikin shekaru kusan 200 da aka haifa a wata ‘kasa ta daban ba Amurka ba.

XS
SM
MD
LG