Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Yana Neman Wanda Zai Nada Shugaban FBI


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

A nan Amurka, hukumomi na nan suna neman mutumin da za’a nada a matsayin sabon shugaban hukumar binciken manyan laifuka ta FBI bayan shugaba Donald Trump ya kori James Comey a satin da ya gabata.

Izuwa yanzu an tattauna da kimanin mutane takwas wadanda ke neman mukamin, kuma shugaba Trump yace kafin ranar Juma’a za’a fadi wanda aka baiwa mukamin, kafin Trump din ya tashi zuwa kai ziyarar sa ta farko a kasashen ketare a matsayin Shugaban kasa.

A daya bangaren kuwa, Shugaban kasar yana ci gaba da shan sukar lamirinsa daga shuwagabanni manyan jam’iyyun siyasan kasar guda biyu (na Democrats da Republicans)

Suna kalubalantar matakan da ya dauka a satin da ya gabata, wanda ya hada da sauya dalilan da yasa aka kori Comey da kuma jerin sakonnin Twitter da yayi na gargadin Comey kada ya kuskura yayi magana da Manema Labarai akan korarsa.

Shugaba Trump yace Comey yayi fatan shi Trump bashi da wasu fayafayen daukan sati da aka dauka na magangannun da suka yi a lokacin tattaunawarsu

A jiya Lahadi, ‘yan majalisar dokoki sunyi kira ga Trump da ya bayar da duk wasu fayafayen Kaset din tattaunawarsu da Comey.

A hirarshi da tashar telebijin ta NBC, dan majalisar Dattawa, Sanata Lindsey Graham na Jam’iyyar Republican yace dole ne fadar White House ta fayyace wa duniya idan akwai wasu kaset-kaset na wannan tattaunawar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG