Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Zai Yarda Da Kudurin Majalisa Kan Kare Yara Bakin Haure


Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya gayawa manyan yan majalisar dokoki a yau Talata cewar zai amince da duk wata doka da majalisa ta yarda da ita na kare dubban yara bakin haure

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya gayawa manyan 'yan majalisar dokoki a yau Talata cewar zai amince da duk kudurin dokar da majalisa ta zartas da ita na kare dubban yara bakin haure daga kora daga Amurka tare da bunkasa tsaro a iyakar Amurka da Mexico.

A wani gagarumin zaman tattaunawa a fadar White House, shugaban yace za a tattauna maganar sabunta harkokin shige da fice na kasar daga baya. Ya kara da cewa ya yi imanin akwai bukatar a gina katanga akan iyakar Amurka da Mexico, amma kuma da alama ya janye daga bukatar cewa a ware kudaden gina katangar nan take.

A wata sanarwar da kakakin fadar White House ta bayar, ta ce, "shugaba Donald Trump ya samu nasarar tattaunawa da bangarori biyu akan sabunta harkokin shige da fice. A tattaunawar da sukayi ta sirri, sun cimma matsayi a kan maida hankali kan duk wata doka da zata taimaka wajen gyara wurare masu muhimmanci guda hudu wadanda suka kunshi tsaron iyaka, DACA, gasar samun Visar Amurka da kuma harkokin shige da ficen kasar."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG