Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dr Daniel Iya: Samar Da Inshorar Kiwon Lafiya Ce Hanya Mafi Dacewa A Najeriya


Dr Daniel Iya, Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Nasarawa
Dr Daniel Iya, Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Nasarawa

Gwamnati Najeriya na shirin fara gudanar da inshorar lafiya a fadin kasar lamarin da masana ke ganin zai taimaka wajan inganta kiwon lafiya da samar da kulawa cikin sauki musamman ga marasa karfi.

A wata tattauwan ta wayar tarho da ma’aikaciyar shashen Hausa na muryar Amurka Grace Alheri Abdu, Kwamishinan lafiya na jihar Nasarawa Dr Daniel Iya, ya bayyana cewa hanya mafi dacewa wajan inganta ayyukan kiwon lafiya, it ace gwamnati ta kebe kudade na musamman domin kula da harkokin lafiyar al’ummar ta.

Da yake bayani, akan tsarin inshorar lafiya da gwamnatin Najeriya ke kokarin samarwa Dr Daniel Iya, ya bayyana cewa hanya mafi dacewa wajan inganta ayyukan kiwon lafiya, ita ce gwamnati ta kebe kudade na musamman domin kula da harkokin lafiyar al’ummar ta sa’annan kuma adadin kudin kudin da babban ma’aikaci zai aje ya banbanta da na karami.

Yayin da yake amsa tambayar da Grace Alheri Abdu, ta yi masa, akan tasirin da inshorar lafiya zai yi a maraya bisa karkara inda ko asibitoci babu, Dr Daniel ya bayyana cewa a yanzu haka gwamnatin Najeriya, na kokarin kafa dakunan shan magani da ake kira primary Health Care, a kowace mazaba, kuamdaga nan za’a fara.

Kasancewa wannan shine karon farko da za a samar da inshorar lafiya a Najeriya, duk da cewa sauran kasashen da suka jima suna amfani da irin wannan inshora na fuskantar kalubale, kwamishinan ya bayyana cewa akwai matakai na musamman da zasu taimaka wajan wayar da kan al’umma a kan yadda za a tafiyar da harkokin inshorar lafiyar.

Saurari cikakkiyar hirar a nan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:40 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG