Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban Mutane Na Tserewa daga Mosul Kasar Iraqi


Mutane dake tserewa daga Mosul
Mutane dake tserewa daga Mosul

Kungiyar rajin kare yara ta Save The Children ta fadi yau Laraba cewa dubban mutane sun tsere daga birin Mosul na kasar Iraki, don su kauce ma farmakin da sojojin Iraki da na Kurdawa ke kaiwa, da zummar sake kwato birnin daga hannun mayakan ISIS.

Kungiyar agajin ta ce mutane wajen 5,000 suka isa wani sanasanin 'yan gudun hijira dake Siriya cikin kwanaki 10 da suka gabata, kuma wai da alamar nawaya za tayi yiwa sansanin yawa yayin da mutane ke kara zuwa.

"Iyalai na ta zuwa ba tare da komi ba illa tufafi kuma ba su samun komai na tallafi," a cewar Tarik Kadir, wanda ke jagorantar sashin Mosul na kungiyar.

Sojojin Amurka sama da 100 ne ke taimaka ma sojojin na Iraki da Kurdawan Peshmerga a yakin na Mosul.

Mai magana da yawun Hedikwatar Tsaro ta Pentagon Navy Capt Jeff Davis ya gaya ma manema labarai jiya Talata cewa sojojin na Amurka na taimakawa ne ma sojojin Kurdawa 10,000 da na Iraki 18,000 da kuma wani rukuni na sojojin Iraki yayin da suke tinkarar mayakan ISIS, wadanda suka ja daga a birni na biyu mafi girma a kasar ta Iraki na tsawon sama da shekaru biyu.

An yi kiyasin akwai mayakan ISIS tsakanin 3,000 zuwa 5,000 a birnin na Mosul. Jami'an Amurka sun ce mayakan ISIS mafi kwarewa na girke a Mosul kuma masu himma ne wajen yaki da kuma akidarsu.

XS
SM
MD
LG