Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban Mutane Suka Fito Bada Jini Don Taimakawa Wadanda Suka Jikata a Harin Las Vegas


Mutanen da suka taru wurin masu bada magani a wurin da aka yi harbi
Mutanen da suka taru wurin masu bada magani a wurin da aka yi harbi

Biyo bayan harbe mutane 59 har lahira da jikata wasu 500 da Stephen Paddock yayi ranar Lahadinda ta gabata, dubban mutane suka tsaya dogon layi a birnin Las Vegas dake Amurka don su bada jininsu domin a taimakawa wadanda suka jikata

A birnin Las Vegas na nan Amurka dimbin mutane sunyi tsaye akan dogon layi har na tsawon awanni takwas domin a dauki jininsu don taimakawa mutanen da suka jikkata a dalilin harin da aka kai jiya, wanda shine hari mafi muni da wani mutum guda shi kadai ya taba kaiwa da bindiga a tarihin Amurka.

An bayyana ‘dan bindigar da suna Stephen Paddock mai shekaru 64 dan asalin garin Mesquite (Meskwit) dake a jihar Nevada, ya bude wuta kan mutane fiye da dubu 22 dake kallon wasan mawaka a jiya Lahadi da daddare kafin ya kashe kansa lokacinda ‘yansanda ke dada matsowa zuwa ga dakin nashi.

Paddock ya bude wutar ne daga dakin otal dinsa dake hawan bene na 32 a otel din Mandalay Bay, wanda ke tsallaken titi daga inda ake gudanar da wasan mawakan.

Mutane 59 ne suka rasa rayukansu, haka kuma wasu 527 sun raunata.

Baturen ‘yan Sandan karamar hukumar Clark, Joe Lombardo, ya ce an samu makamai iri-iri har guda 16 a dakin maharin dake otel din, da bindigogi 18 hade da nakiyoyi da kuma dubban harsashai a gidan maharin dake garin Mesquite.

Shguaban Amurka Donald Trump ya jagoranci shirun mintoci da al’ummar Amurka suka yi don nuna juyayi a fadar White House.

Haka kuma Trump ya kuma bayar da umarnin a sassauta tutucin Amurka a duk fadin kasar, ya kuma shirya zai je birnin Las Vegas gobe Laraba domin ganawa da ma’aikatan da suka kai daukin gaggawa da kuma wadanda lamarin ya shafa da iyalansu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG