Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban Mutane Sun Yi Zanga-zanga a Kasar Belarus


Masu Zanga-zanga a kasar Belarus
Masu Zanga-zanga a kasar Belarus

Dubban mutane sun yi cincirindo a babban birnin kasar Belarus a jiya Lahadi, suna kira ga shugaba Alexander Lukashenko ya sauka daga karagar mulki biyo bayan tarzoma da aka shiga kan zaben da ake takaddama a kai cikin cikkaken tsaron soja a birnin.

Masu zanga-zanga da yawan su sun rike ko kuma sanya sutura mai launin Ja da Fari, alamar jam’yiyar adawa, suna cewa “Yanci” da “ba zamu manta ba” yayin da suke tattaki a birnin na Minsk. Sun taru na dan lokaci kadan a kusa da fadar shugaban kasar kafin su watse ba tare da tashin hankali ba.

Yayin da kafar yada labarai ta kasar ta sanar da adadin masu zanga zanga dubu 200,000 ne, kafafen watsa labarai da suke bayan kungiyoyin hamayya, sun yi kiyasin cewa wadanda suka shiga zanga-zangar sun kai dubu 100,000 a cewar kamfanin dillacin labaran kasar Faransa.

Tun ran 9 ga watan Agusta a ka fara zanga zanga, yayin da Lukashenko ya yi ikirarin lashe kashi 80 cikin dari, na kuri’un da aka kada. Jam’iyyun adawa sun yi zargin cewa an tafka magudi.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG