Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban Mutane Sun Yi Zanga-zanga a Kasar Togo


Masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a kasar Togo
Masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a kasar Togo

Dubban mutane sun yi zanga zanga a duk fadin kasar Togo jiya Laraba, suna bukatar kawo karshen mulkin shekara da shekaru da shugaban kasar Faure Gnassingbe da iyalin sa suke yiwa kasar.

Shugabanin jam’iyun masu hamaiya na kasar ne suka bukaci dubban mutane da su fatsama titinan Lome baban birnin kasar da wasu biranen kasar, su bukaci shugaba Gnassinge ya sauka daga kan ragamar mulkin bayan wa’adinsa ya kare a shekara ta dubu biyu da ashirin idan Allah ya kaimu. Haka kuma sun bukaci a yiwa tsarin mulkin kasar kwaskwarima domin kayade waadin mulkin shugaba,

A alif dari tara da casa’in da biyu aka zartar da wata doka data tanadin wa’adin biyu wa shugaban kasa, to amma mahaifin shugaba Gnassingbe, marigayi Gnassingbe Eyadema ya soke wannan doka bayan shekaru goma.

Zanga zanga makamancin wannan da aka yi a watan Augusta ta buge da zama tarzoma harma jami’an tsaro suka kashe mutane biyu

A shekara ta dubu biyu da biyar shugaba Faure Gnassingbe ya dare kan ragamar mulki bayan rasuwar mahaifinsa wanda ya share shekaru talatin da takwas yana jan ragamar mulkin kasar Togo.

A ranar Talata Majalisar Ministocin kasar tayi na’am da wata shawarar da aka gabatar na maida da kayade wa’adin mulkin shugaban kasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG