Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kenya Za Ta Sake Zaben Shugaban Kasa Ranar 17 Ga Watan Oktoba


Akwatunan jefa kuri'a a zaben a Nairobi, ranar zaben 9 ga watan Agustan 2017
Akwatunan jefa kuri'a a zaben a Nairobi, ranar zaben 9 ga watan Agustan 2017

Bayan ce-ce-ku-ce da aka yi ta yi tsakanin bangaren shari'ar Kenya da gwamnatin shugaba Uhuru Kenyatta, hukumar zaben kasar ta ce a watan Oktoba mai zuwa za a sake zaben shugaban kasar da kotun koli ta soke.

Hukumar zaben kasar Kenya ta ce ranar 17 ga watan Oktoban wannan shekarar za a sake gudanar da zaben shugaban kasa da aka soke.

Hukumar ta ce ta saka wannan ranar ce domin tabi umurnin da babban kotun kasar ta bayar, biyo bayar rusa zaben da ta yi a watan da ya gabata sakamakon magudin da ake zargin an yi wajen kirga kuri’un da aka jefa.

Wannan ya sa ta ce a gudanar da zaben bayan kwanaki 60 wato cikin watanni biyu kenan.

Sanarwan da hukumar zaben kasar ta fitar ta ce sunayen shugaba mai-ci Uhuru Kenyatta da mataimakinsa da kuma na Raila Odinga da na mataimakinsa ne kawai za su kasance a katin jefa kuri’a a zaben na watan gobe.

Idan ba a manta ba, an ayyana shugaban da ke kan karagar mulki wato Kenyata a matsayin wanda ya lashe zaben da banbancin kuri’u har miliyan 1.4.

Amma shugaban ‘yan adawa Raila Odinga na gamayyar jam’iyyun adawa ta NASA, ya ce an tafka magudi, lamarin da ya sa ya kai maganar kotu wadda daga bisani ta soke zaben bayan da kotun ta tabbatar zarginsa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG