Accessibility links

Dubban mutane sun yi zanga zanga a Misira


Misirawa sun yi tururuwa a Dandalin yanci dake birnin Alkahira

Dubban Misirawa sun yi dafifi a kan titunan kasar jiya asabar da dare, suna zanga zangar kin amincewa da hukumcin da aka yanke a shari’ar tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak

Dubban Misirawa ne suka yi dafifi a kan titunan kasar jiya asabar da dare, suna zanga zangar kin amincewa da hukumcin da aka yanke a shari’ar tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak, da tsohon ministan harkokin cikin gida Habib al-Adly da kuma wadansu manyan jami’an tsaro shida.

An sami hambararren shugaban kasar da laifi sakamakon rawar da ya taka a kashe daruruwan masu zanga zangar kin jinin gwamnati a makon farko da aka fara zanga zanga cikin watan Fabrairu shekara ta dubu biyu da goma sha daya, da ta tilasta barin mulkinsa. An yankewa Mr. Mubarak hukumcin daurin rai da rai. Masu shigar da kara sun nemi a yanke mashi hukumcin kisa, sai dai alkalin da ya jagorancin shari’ar yace ko da yake Mr. Mubarak bai hana kisan ba, bashi da hannu kai tsaye a kisan. Ana kyautata zaton lauyoyin Mr. Mubarak zasu daukaka kara.

An sami ministan harkokin cikin gida da yake da matukar bakin jinni da laifi, shima aka yanke mashi hukumcin daurin rai da rai, yayinda aka wanke manyan jami’an tsaron kasar.

Kotun ta kuma wanke Mubarak da ‘ya’yanshi biyu Gamal da Alaa da kuma wadansu mutane, da aikata laifin zarmiya da ake tuhumarsu a kai.

Masu zanga zanga sun yi dafifi a biranen alkahira, da Alexandria, da Suez da sauran biranen kasar Masar. Masu zanga zanga a alkahira sun yi dafifi a dandalin Tahrir, cibiyar juyi juya halin, suna nema a sake shari’ar a kuma yankewa Mr. Mubarak hukumcin kisa. Yayinda kuma suke nuna rashin amincewa da wanke jami’an tsaron kasar da kotu tayi.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG