Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban 'Yan Gudun Hijira Suka Shiga Kasar Slovenia


'Yansandan Slovenia suna yiwa 'yan gudun hijira jagoranci zuwa shiga garin Dobova

Yawan 'yan gudun hijira dake kwararawa cikin kasar Slovenia daga iyakarta da kasar Croatia ya tilasta mata daukan matakin tura 'yansanda da sojoji bakin iyakar da nufin takaita bakin hauren da ke shiga kasar.

Dubban ‘yan gudun hijira ne suka shiga kasar Slovenia tun ranar Asabar, wanda hakan ya tursasawa kasar daukar matakintakaita kwararar bakin ta kan iyakarsu daga kudancin kasar.

Jami’an Slovenia sunce kimanin ‘yan gudun hijira dubu hudu ciki har da jarirai da kananan yara ne suka shiga kasar a jiya Talata daga Croatia.

Wannan adadi kuma kari ne akan mutane dubu takwas da suka isa kasar a ranar Litinin. Shugaban kasar Borut Pahor yace karin ‘yan sanda za su isa kan iyakar kasarsa da Croatia.

Sannan za su kai karin sojoji duk domin shawo kan lamarin na kwararowar bakin hauren da ya wuce kima.

Bidiyo

Ko Kun San Irin Makaman Da Sojoji Ke Amfani Da Su Wajen Yaki Da 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara?
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:31 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG