Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban 'Yan Mali Sun Yi Zanga-Zangar Goyon Bayan Juyin Mulki


Kakakin sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Mali, Leftana Amadou Konare, a tsakiya, kewaye da masu gadinsa a lokacin da ya halarci gangamin nuna goyon baya ga juyin mulkin domin yin jawabi, Laraba 28 Maris 2012 a Bamako, babban birnin kasar.

Da alamun kawunan al'ummar Mali sun rabu game da wannan juyin mulkin, wanda ya janyo tofin Allah tsine daga kasashen waje tare da bukatar maido da gwamnati irin ta tsarin mulki.

Dubban jama'a sun yi maci yau laraba a titunan babban birnin kasar Mali domin nuna goyon bayansu ga sojojin da suka kwaci mulkin kasar, yayin da kasashen ketare suke kara nuna adawa ga shugabannin sojan.

Da alamun kawunan al'ummar Mali sun rabu game da wannan juyin mulkin, wanda ya janyo tofin Allah tsine daga kasashen waje tare da bukatar maido da gwamnati irin ta tsarin mulki.

A martani na baya-bayan nan ga juyin mulkin, Kungiyar Tarayyar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CDEAO, ta yi barazanar kafa takunkumi, ko kuma daukar matakan soja idan bukatar hakan ta taso.

Kungiyar ta kasashen Afirka ta Yamma ta ce zuwa gobe alhamis zata tura shugabannin kasashe akalla 5 zuwa Mali domin tattauna yadda za a maido da shugaban kasar na halal da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya, Amadou Toumani Toure, da gwamnatinsa.

A bayan taron gaggawar da ta yi ranar talata, kungiyar ta ECOWAS mai wakilai 15 ta ce tana nazarin dukkan matakan da za a iya dauka, kuma akwai rundunar kiyaye zaman lafiya da take ajiye idan za a bukaci girka ta a kasar.

XS
SM
MD
LG