Accessibility links

Dubun Dubatan Misrawa Suka Hallara A Dandalin Tahrir Don Zanga Zanga

  • Aliyu Imam

Misrawa suke zanga zanga a dandalin Tahrir.

Dubun Dubatar masu zanga-zanga ne yau Juma’a suka hadu a dandalin Tahrir suna la’antar matakan da rundunar sojin Misra ke dauka na juyin mulki a fakaice.

Dubun Dubatar masu zanga-zanga ne yau Juma’a suka hadu a dandalin Tahrir suna la’antar matakan da rundunar sojin Misra ke dauka na juyin mulki a fakaice tare da yin kiran da a gaggauta bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a karshen mako.

Idan za’a iya tunawa, jiya hukumar zaben kasar Misra tace an jingine sanarwar da aka shirya bayarwa ta sakamakon zaben shugaban kasa bisa dalilin cewar anyi zargin tafka magudi a zaben don haka sai an bincika.

Jam’iyyar Muslim Brotherhood tayi gargadin tada tarzoma muddin aka murde sakamakon zaben aka hana wakilinsu Muhammad Morsi hawa kujerar shugaban kasa.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG