Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubun Masu Yiwa Yara Fyade a Adamawa Ya Cika


Wasu dake yiwa yara mata fyade, a yankin Mubi, Jihar Adamawa

An dade ana neman warware bakin zaren matsalar fyade da ake yiwa yara mata an 'yan kasa da shekaru 15 kafin hukumar Civil Defense ta ci karo da wata kungiyar mutanen da suka yi kamarin suna wajen aikata mummunar dabi'ar da shekarunsu ya kama daga 29 zuwa 42

Ba tun yau ba ne ma dai ake zargin cewa akwai gungun wasu da suka kware wajen yiwa kananan yara fyade a yankin Mubi,wanda kuma aka dade ana fakonsu to amma sai a wannan karon ne dubun su ya cika,inda suka fada tarkon jami’an rundunar tsaron farin kaya ta Civil Defense.

Da a ke nunawa manema labarai wadanda aka kaman a shedikwatar hukumar dake Yola, kakakin rundunan tsaron farin kaya ,Civil Defense, Suleiman Baba ya ce binciken jami’an asibiti a Mubi da kuma bahasin wadanda aka yiwa fyaden da kuma mabarnatan duk sun tabbatar da cewa yara kanana hudu ne suka yiwa fyade ,kuma masu kananan shekaru daga 10 zuwa shekaru 12.

Suleiman Baba ya ce dubun wadanda ake zargin ya cika ne bayan da yan uwan wadannan yara suka tsaigunta wa jami’an tsaron ,inda ya ce ma za’a gurfanar da wadanda ake tuhuman gaban kotu.

Wadanda aka kaman dai sun ko hada da Abdullahi Ibrahim mai kimanin shekaru 32, sai Musa Mohammed (31), Bakura Mohammed (39), Joseph John (29), da kuma Mohammed Musa (42).

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG