Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duk da Ikirarin Kamma Raba Katin Zabe a Jihar Yobe da Hukumar Zabe Tayi Wasu Basu Samu Katin Ba


Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, (INEC) Farfasa Attahiru Jega y.
Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, (INEC) Farfasa Attahiru Jega y.

Yayin da hukumar zabe mai zaman kanta ko INEC ke ikirarin kamma raba katin zabe a jihar Yobe wasu al'ummar karamar hukumar Gulani sun ce su basu samu katin ba kuma babu wani jami'i da ya je wurinsu.

Wani mazaunin garin ya shaidawa wakiliyar Muryar Amurka cewa su har kawo karshen wa'adin da hukumar zabe ta bada basu ga wani jami'in zabe ba balantana ya raba masu katin.

Mutanen garin sun ce sun zauna suna jiran abun da Allah zai yi domin babu inda zasu iya kai kuka. Kamar yadda hukumar zabe ta sanar duk wanda bashi da katin ba zai iya jeka kuri'a ba. Mutanen suna rokon ko za'a kara lokaci domin a samu a kawo garesu.

Shugaban hukumar zaben ko INEC a jihar Yobe Malam Sadiq Musa ya bayyanawa wakiliyar Muryar Amurka lokacin da ta tuntubeshi akan lamarin sai yace su sun gama aikinsu bisa ga wa'adin da hukumar ta kasa ta basu. Abun da suke jira shi ne jami'ansu su kawo masu kidigdigan iyakacin katin da suka bayar kana su tura zuwa Abuja. Akan ko shirin ya samu nasara a jihar Yobe sai Malam Sadiq yace an samu nasara domin mutane sun fito har ma sun bashi mamaki.

Dangane da kananan hukumomin Gulani da Gujiba wadanda suka ce basu samu katin ba sai yace lokacin da suke yin shiri jami'an tsaro sun fada masu cewa sabili da wasu dalilan tsaro ba zasu iya shiga kananan hukumomin Gulani da Gujiba ba. Su dakata sai tsaro ya inganta kana suna iya shiga su raba katin. Yace katin zabensu suna nan kuma za'a basu kamar yadda aka ba kowa.

Kawo yanzu dai jihar Yobe ita ce ta farko da hukumar zabe ta raba kati cikin jihohi ukun dake karkashin dokar ta baci.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG