Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duk da Tallafin Gwamnatin Tarayya Jihar Adamawa Bata Biya Tsoffin Ma'aikata Ba


Jerin gwanon ma'aikata jihar Adamawa
Jerin gwanon ma'aikata jihar Adamawa

Rashin biyan ma'aikata musamman tsoffin ma'aikata ya sa kungiyar kwadago reshen jihar Adamawa yin jerin gwano domin nuna fushinsu

Kungiyoyin kwadago sun nemi gwamnmatin tarayya ta rika ware kaso na musamman domin biyan ‘yan kwadago da tsoffin ma’aikata hakkokinsu nan gaba daga tallafin da ta ke baiwa jihohi.

Kungiyoyin kwadagon sun dauki wanna matsayin nebiyo bayan jawabin shugaba Mohammadu Buhari ga ‘yan Najeriya albarkacin zagayowar ranar samun yancin kai shekaru hamsin da bakwai da suka gabata inda ya bada sanarwar cewa gwamnatin tarayya ta baiwa jihohin tallafi naira tiriliyan daya da miliyan dubu dari shida da arba’inda biyu tun daga shekarar 2015.

Muryar Amurka ta yi nazarin yadda jihohin Adamawa da Taraba da suka anfana da sama da naira biliyan goma sha biyar da kuma naira biliyan takwas ko waccensu amma duk da haka ma’aikatansu na bin gwamnatocin Adamawa da Taraba albashin watanni hudu zuwa shida. Wannan al’amarin ya fi shahuwar ma’aikatan kananan hukumomi, jam’an kiwon lafiya da malaman firamare.

Baki ya zo daya kan kasawar da gwamnatocin suka yi na rage bashin kudin sallama ga tsoffin ma’aikata lokacin da shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya rassan jihohin Adamawa da Taraba, Maina Dauda da Peter Gambo ke bayanin yadda aka sarrafa tallafin a jihohinsu.

Da yake bayanin yadda ‘ya’yan kungiyarsa suka anfana daga kaso na sama da biliyan goma sha biyar da gwamnatin jihar ta karba, shugaban kungiyar masu kabar fansho ta kasa reshen jihar Adamawa, Komrad Samson Almuru ya ce abin takaici ne a ce Naira biliyan daya kacal aka ware don rage bashin tsoffin ma’aikatan gwamnatin jiha da na kananan hukumomi na sama da biliyan ashirin da suke bin ta.

Lokacin da Muyar Amurka ta tuntubi shugaban hukumar kula da masu karbar fansho ta jihar Adamawa Alhaji Abubakar Njidda Sarau ya shaidawa wakilinmu Sanusi Adamu cewa gwamnatin jihar ta hana shi yi wa ‘yan jarida bayanin yadda hukumarsa ke sarrafa kudade da ke shiga asusun ta.

Saurari karin bayanin rahoton wakilin namu, Sanusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG