Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dukkan Mayakan Boko Haram Da Ake Tsare Da A Gidan Yarin Kuje Sun Tsere: Magashi

Dukkan Mayakan Boko Haram Da Ake Tsare Da A Gidan Yarin Kuje Sun Tsere: Magashi
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:51 0:00

‘Yan tawayen sun kai hari gidan yarin Kuje da ke Abuja a daren ranar Talata ta hanyar amfani da “bama-bamai masu girman gaske,” inda suka kashe wani mai gadi a bakin aiki, a cewar Shuaib Belgore, sakatare na ma’aikatar harkokin cikin gida ta Najeriya. An kona motoci da barna.

Akalla fursunoni 600 ne suka tsere, a cewar jami'ai a ranar Laraba, inda suka dora alhakin harin kan 'yan tawaye masu tsattsauran ra'ayi. Amma kimanin fursunoni sama da 400 ne aka sake kamawa, in ji hukumomi.

Ministan tsaron Najeriya, Bashir Salihu Magashi, ya ce dukkan mayakan Boko Haram da ake tsare da su a gidan yarin Kuje sun tsere.

XS
SM
MD
LG