Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dukkan Mutanen Dake Cikin Jirgin Saman Fasinja Na Rasha Da Ya Fadi Sun Mutu


Ma'aikatan agaji na Rasha a wurein da jirgin saman fasinja ya fado lahadi
Ma'aikatan agaji na Rasha a wurein da jirgin saman fasinja ya fado lahadi

Jami'an Rasha sun fada a yau lahadi cewa dukkan mutane 71 dake cikin wani jirgin saman fasinja na kasar Rasha sun mutu a lokacin da jirgin ya fadi a kusa da birnin Moscow.

Ofishin binciken hatsarin ababen hawa na kasar Rasha ya ce, "akwai fasinja 65 da kuma ma'aikata su 6 a wannan jirgi da ya fadi, kuma dukkansu sun mutu." Akwai yara kanana su 3 a cikin wadanda suka mutun.

Wannan jirgi da aka kera shi shekaru 7 kacal da suka shige, ya bace daga na'urar hango jirage a sama, jim kadan bayan tashinsa daga filin jirgin saman Domodedovo, wanda shine na biyu wajen girma a babban birnin kasar. Wani shafin dake bin sawun zirga zirgar jiragen sama mai suna FlightRadar24 yace jirgin ya subuto kasa da saurin mita dubu 6 da 700 cikin minti daya, 'yan dakikoki kafin ya ci karo da doron kasa.

Wannan jirgin sama kirar An-148 na kamfanin safarar jiragen saman Saratov Airlines, ya tashi ne a kan hanyar zuwa birnin Orsk a lokacin da ya fado a kusa da Argunovo, mai tazarar kilomita 80 a kudu maso gabas da birnin Moscow.

Har yanzu ba a san musabbabin faduwar wan nan jirgi ba, amma kafofin yada labarai na Rasha sun ce masu bincike sun gano daya daga cikin na'urorin tattara bayanai guda biyu na jirgin, koda yake ba a san ko na'urar nade maganganun matuka ne, ko kuma mai auna yadda sassan jirgin suke aiki ba.

Ministan sufuri na Rasha, Maxim Sokolov ya shaidawa 'yan jarida lahadin nan cewa lokaci bai yi na sanin takamammen abinda ya janyo wannan hatsari ba, amma kuma hukumar kula da zirga zirgar jiragen saman farar hula ta kasar tana bin deiddigin dukkan abubuwan da ka iya kawo faduwar wannan jirgi.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya aike da sakon ta'aziyya da kuma jimaminsa ga iyalan wadanda suka rasu a wannan hatsarin, in ji wata sanarwar da kakakinsa Dmitry Peskov, ya bayar.

Shugaba Donald Trump na Amurka ya bi sahun shugabannin duniya wajen aikewa da sakon ta'aziyya ga shugaba Putin da al'ummar Rasha a dangane da wannan hatsarin.

Wannan jirgin fasinja ya fadi a wani wurin da yake cike da dusar kankara, wadda ta jinkirta isar ma'aikatan agaji zuwa wurin. Ala tilas sai da suka ajiye motocinsa suka karasa da kafa.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG