Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duniya Ta Sami Koma Baya Akan Cin Hanci Da Rashawa


Kungiyar dake sa ido kan batun cin hanci da rashawa, da alakar rashin daidaito tsakanin al’umma, da zarmiya a gwamnati, ta fitar da rahotonta na shekara-shekara, inda ta bayyana cewa, mutane suna zaben shugabannin da suka yi alkawarin yaki da cin hanci da rashawa wadanda mai yiwuwa su sa lamarin ya kara muni.

Rahoton na shekara ta dubu biyu da goma sha shida yace, an sami koma baya a kasashe da dama a maimakon ci gaba a fannin yaki da cin hanci da rashawa.

Kasashen dake kan gaba a fannin yaki da cin hanci da rashawa sun hada da Denmark da New Zealand, da Sweden da kuma Finland. Bisa ga rahoton, wadannan kasashen suna gudanar da tsarin mulki irin na kofa bude, da ba ‘yan jaridu damar gudanar da ayyukansu ba tare da tsangwama ba, da kuma sakarwa fannin shari’a kota ya gudanar da ayyukansa.

Rahoton ya kuma kara da cewa, wadannan kasashen suna ba ‘yan kasa damar nema da samun bayanai dangane da yadda ake kashe kudin al’umma.

Kasar Somaliya ta zo ta karshe a matsayin kasar da aka fi cin hanci da rashawa shekaru goma jere. Rahoton ya bayyana damuwa dangane da rashin gaskiya a zaben ‘yan majalisar dokokin kasar, da kuma zaben shugaban kasar da aka dage har sau uku.

An gudanar da binciken ne a kasashe dari da tamanin da shida na duniya, da binciken kungiyar ya nuna kashi sittin da tara cikin dari na kasashen sun sami maki kasa da hamsin cikin dari bisa a sikelin nuna munin lamarin.

XS
SM
MD
LG