WASHINGTON D.C. —
A ranar Larabar da ta gabata ne ‘yan majalisar dokokin Amurka, suka gudanar da wani zaman sauraren bahasi, wanda ya mayar da hankali kan abin da suka kira; tabarbarewar tsarin mulkin dimokradiyya da ake gani a wasu sassan kasashen da ke kudu da hamadar Sahara a nahiyar Afirka – abin da suka ce, yana tasiri akan tattalin arzikin yankin da fannin ilimi da na lafiya. Batun da shirin Duniyar Amurka na wannan mako ya yi dubi a kai kenan.
Facebook Forum