Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dutse Mai Aman Wuta Ya Sake Kashe Mutane Fiye Da Hamsin


Hoton Dutsen Merapi daga cikinw ani jirgin sama dake wucewa ta kusa da inda wannan dutse ke aman wuta da toka mai tsananin zafi

Mutane kimanin dari daya ke nan suka mutu a sanadin wannan dutse dake tumbudin toka da hayaki da narkakken dutse a kasar Indonesiya

Ma'aikatan asibiti a kasar Indonesiya sun ce dutsen Merapi mai aman wuta ya sake yin tumbudi, ya kashe karin mutane akalla 54 ya zuwa safiyar jumma'a.

Wasu mutane kimanin saba'in sun ji rauni, akasarinsu kuna, a bayan da wannan dutse ya fara tuttudo da hayaki da toka mai tsananin zafi da misalin karfe 12 na daren alhamis har zuwa asubahin jumma'a. Jami'ai su na kyautata zaton adadin wadanda suka mutu zai zarce haka a yayin da masu aikin ceto da ke samun tallafin sojoji, suke tono gawarwaki daga cikin tokar da ta rufe su.

Mace-mace na baya-bayan nan sun sa adadin wadanda suka mutu tun daga lokacin da wannan dutse ya fara aman wuta a ranar 26 ga watan Oktoba, zuwa kimanin 100.

Dutse Mai Aman Wuta Ya Sake Kashe Mutane Fiye Da Hamsin
Dutse Mai Aman Wuta Ya Sake Kashe Mutane Fiye Da Hamsin

Jami'an Indonesiya sun fadada yankin da aka ayyana a zaman mai hatsari a kewayen dutse zuwa kilomita 20 a kewayensa, sun kuma bayar da umurnin da a matsa da sansanonin gaggawa da aka kakkafa a kara yin nesa da su daga inda wannan dutse yake.

Ma'aikatar sufuri ta Indonesiya ta gargadi matuka jiragen sama da su yi nesa da wannan dutse mai aman wuta wanda a yanzu haka yake tuttudo toka mai tsananin zafi da kuma iskar gas.

XS
SM
MD
LG