Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Falasdinawa Sun Sake Barazanar Ayyana Kasarsu A Majalisar Dinkin Duniya


Shugaban Falasdinawa, Mahmoud Abbas

Shugaban Falasdinawan yace bai kamata firayim ministan Isra'ila yayi musu kashedi game da bin radin kansu wajen ayyana kasar Falasdinu ba.

Shugaban Falasdinawa, Mahmoud Abbas, yace bai kamata firayim ministan bani Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya nemi ja masa kunne a kan kada yayi gaban kansa ya ayyana kafa kasar Falasdinu ba, a yayin da ita kanta Isra’ila ta yi gaban kanta tana giggina gidaje ma yahudawa a Yankin Yammacin Kogin Jordan.

Shugaba Abbas ya fada litinin cewa ganin yadda Isra’ila take kakkafa shingaye tare da gina gidaje ma yahudawa a yankunan Falasdinawa da ta mamaye, bai kamata a ce Mr. Netanyahu ne zai yi ma Falasdinawa lacca a kan kada su dauki matakan neman Majalisar Dinkin Duniya da ta amince da kasar Falasdinu ‘yantacciya ba.

Batun gina ma yahudawa gidaje a yankunan Falasdinawa da Isra'ila ta mamaye a yakin gabas ta tsakiya na 1967, shi ne ya kawo cijewar yunkurin wanzar da zaman lafiya na baya-bayan nan.
Batun gina ma yahudawa gidaje a yankunan Falasdinawa da Isra'ila ta mamaye a yakin gabas ta tsakiya na 1967, shi ne ya kawo cijewar yunkurin wanzar da zaman lafiya na baya-bayan nan.

A can baya, jami’an Falasdinawa sun bayyana yiwuwar tinkarar Majalisar Dinkin Duniya domin neman ta amince da yankunan da Isra’ila ta kwace a yakin gabas ta tsakiya na 1967, watau Yankin Yammacin Kogin Jordan, da Zirin Gaza da kuma Gabashin birnin Qudus, a zaman kasar Falasdinu ‘Yantacciya.

A ranar lahadi Mr. Netanyahu ya soki wannan matakin, yana mai fadin cewa tattaunawa kai tsaye ita ce kadai hanyar da Falasdinawa suke da ita ta cimma zaman lafiya na zahiri da Isra’ila. Yace duk wani yunkurin kaucewa tattaunawa ta hanyar tunkarar hukumomi na kasa da kasa ba zai haifar da abinda Falasdinawan ke so ba.

XS
SM
MD
LG