Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ECOWAS Ta Dage Wasu Takunkumai Ga Kasashen Nijar Da Mali Da Burkina Faso


Bola Tinubu
Bola Tinubu

Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirta ta Yamma, ECOWAS, ta amince da ta dage wasu takunkumai da ta kakabawa kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso da kuma Guinea.

An gabatar da kudirin ne yayin wani taron kungiyar na musamman kan zaman lafiya da siyasa da kuma yanayin tsaro a yankin kasashen ECOWAS a ranar Asabar a Abuja.

Sai dai kungiyar kasashen yankin ta ce takunkumin siyasa da aka kakabawa Nijar zai ci gaba da kasancewa, amma ta dage wasu takunkumai na hada-hadar kudade da na tattalin arziki da aka kakabawa Guinea da wasu takunkumai da aka kakabawa Mali.

Wadannan kasashe dai sun fuskanci fushin kungiyar ECOWAS, tun bayan da sojoji suka hambarar gwamnatocin fararen hula a kasashen, inda ta kakaba musu takunkuman kan karya tattalin arziki da siyasa.

A karshen watan Yulin bara ne dai sojoji suka hamabarar da gwamnatin shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohamed daga kan karagar mulki, lamarin da ya janyo barazanar daukan matakin soji daga kungiyar ECOWAS.

A karshen watan Janairu ne kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar da ke karkashin mulkin soja suka ba da sanarwar hadin gwiwa ta ficewa daga sahun kasashe mambobin ECOWAS, sakamakon abin da suka kira rashin gamsuwa da yadda kungiyar ta kauce wa ainahin turbar da aka kafa ta.

Shugabannin kungiyar ECOWAS sun yi Allah wadai da ficewar kasashen uku daga kungiyar.

Abin jira a gani shi ne ko wannan matakin zai sa kasashen zu janye aniyarsu ta ta ficewa daga ECOWAS.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG