Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ECOWAS Ta Janye Takunkumin Karya Tattalin Arzikin Da Ta Sanya Wa MALI


Shugabannin Kasashen Afirka Ta Yamma Sun Gabatar Da Wani Taro Karkashin Kungiyar ECOWAS
Shugabannin Kasashen Afirka Ta Yamma Sun Gabatar Da Wani Taro Karkashin Kungiyar ECOWAS

A ranar Lahadi ne Shugabannin kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma ta ECOWAS suka dage takunkumin da suka kakabawa kasar Mali, bayan da shugabannin sojin kasar suka gabatar da kudurin mika mulki ga farar hula nan da watanni 24 tare da fitar da sabuwar dokar zabe.

ACCRA, GHANA - Shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma ko ECOWAS a takaice, sun hadu a Accra babban birnin kasar Ghana ranar Lahadi 3 ga watan Yuli domin tattaunawa a kan yadda za a tabbatar da mulkin farar hula a kasashen Mali, Guinea da Burkina Faso.

A wani taron manema labarai, Shugaban ECOWAS Jean-Claude Kassi Brou ya bayyana cewa an dage takunkumin da aka sanya wa kasar Mali.

“Bayan zaman, shugabannin kasashen sun yanke hukuncin dage duk takunkumin karya tattalin arziki da na kudi da muka sanya wa Mali a ranar 9 ga watan Janairu na shekarar 2022,” a cewar Kassi.

Kassi ya kara da cewa sun kuma yanke shawarar ci gaba da sanya takunkumi kan daidaikun mutane da kuma dakatar da Mali daga kungiyar ECOWAS har sai kasar ta koma mulkin dimokradiyya.

Mun kuma yanke shawarar cire takunkumin da muka sanya na janye jakadun kasashen kungiyar ECOWAS a Mali,’ hakan na nufin jakadun kasashen Afrika ta yamma da ke Mali za su dawo domin su ci gaba da harkokin jakadanci.

Kasar Mali, wacce ta yi juyin mulki a watan Agustan 2020 da kuma Mayun 2021, ta kasa biyan sama da dala miliyan 300 na basussukan da ake binta saboda takunkumin.

Shugaba Jean-Claude Kassi Brou ya kara da cewa an dage takunkumin da aka sanya wa kasar Burkina Faso bayan doguwar tattaunawa, inda gwamnatin mulkin sojin kasar ta amince da wa'adin shekaru biyu na komawa mulkin dimokradiyya daga ranar 1 ga Yulin 2022, sabanin watanni 36 da suka bada da farko.

Masanin tattalin arziki Hamza Adam Attijjany ya nuna cewa dage takunkumin zai yi matukar kawo walwalar harkokin tattalin arziki ga wadannan kasashen da ma sauran kasashen Afrika ta yamma musamman a fannin kasuwancin dabbobi da ya durkushe sabili da rufe iyakokin kasashen.

Sai dai shugabannin ECOWAS sun yi watsi da shirin mika mulki ga farar hula nan da shekaru uku da shugabannin Guinea da suka yi juyin mulki a watan Satumba suka yi. Suka ce lallai sai gwamnatin Guinea ta kawo sabon jaddawalin koma wa ga mulkin farar hula a karshen watan Yuli ko kuma su fuskanci takunkumin karya tattalin arziki.

An kuma nada tsohon shugaban kasar Benin, Yayi Boni a matsayin sabon mai shiga tsakani, inda shugabannin suka bukaci gwamnatin mulkin Guinea ta yi aiki da shi tare da gabatar da wani sabon jaddawalin cikin gaggawa.

Saurari rahoton Idris Abdallah Bako

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
XS
SM
MD
LG