Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ECOWAS Tace Babu Abun da Zai Hana Aiwatar da Tsarin Mulkin Gambia


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari dake jagorantar kwamitin ECOWAS akan rikicin siyasar Gambia
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari dake jagorantar kwamitin ECOWAS akan rikicin siyasar Gambia

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari shi ne yake jaroran kwamitin ECOWAS na warware rikicin Gambia ko ta halin kaka har da ma yin anfani da karfin soji idan shugaban kasar Yahya Jammeh ya cigaba da yin turjiya

Kakakin fadar shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya yiwa Muryar Amurka karin bayani akan matsayin kwamitin kungiyar ECOWAS wadda ta kunshi kasashen yammacin Afirka.

Malam Garba Shehu yace kungiyar ECOWAS da kwamitin shugaba Muhammad Buhari sun jaddada cewa babu abun da zai hana a aiwatar da abun da tsarin mulkin Gambia ya tanada ba. Yace wannan kuma yana nufin idan an samu an yishi a cikin ruwan sanyi, a diflomanciyance da kyau. Idan kuma ba'a samu ta cikin ruwan sanyi ba komi na iya biyowa.

Inji Malam Garba babu abun da aka kawar daga tebur da aka ce ba zai faru ba, wato idan ta kama a yi anfani da karfin soji za'a yi.

A cewar kwararre akan sha'anin diflomasiya kuma tsohon jakadan Najeriya a kasar Sudan Suleiman Dahiru yace anfani da karfin soja ya zama wajibi. Yace ya yadda a yi anfani da karfin soja saboda Yahya Jammeh bashi da niyyar sauka daga mulkin da ya kwashe shekaru 22 yana yi. Yace Gambia kasa ce karama kuma duk sojojin kasar basu wuce dubu daya ba saboda haka za'a kawar da shugaban ba tare da matsala ba.

Wani Dr Umar Ardo tsohon malami a kwalajin horas da hafsoshin sojojin Najeriya yace shi bai amince da yin anfani da karfin soja ba domin kasar Gambia karama ce. Yace Najeriya na cikin matsala. Sojojinta na fada ko ta ina cikin kasar sannan kuma ace za'a kaisu waje su yi fada akwai matsala. Yace ko Senegal kawai aka ce ta yiwa kasar Gambia kawanya nan da nan za'a rusa karfin kasar ta ba sai an yi anfani da soji ba.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00

XS
SM
MD
LG