Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EDO: Gwamna Obaseki Zai Koma PDP Ne?


Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki
Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki

Sa'o'i kadan bayan da gwamnan jihar Edo a Najeriya Godwin Obaseki ya fice daga jam'iyya mai mulki ta APC, an fara rade-raden cewa zai koma PDP ne.

Jaridar Punch ma ta rawaito cewa shugaban jam'iyyar PDP a EDO Tony Aziegbemi ya tabbatar da gaskiyar maganar.

A cewarsa, gwamnan tare da wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar ta APC zasu dawo PDP nan ba da jimawa ba.

Hakan na faruwa ne jim kadan bayan da gwamnan ya gana da shugaba Buhari a fadar gwamnati da ke Abuja, kafin daga baya ya bayyana cewa ya Fice daga jam'iyyar.

Ya ce "zai koma wata jam'iyya ne domin ya samu fitowa takara a wa'adi na biyu."

A cikin makon da ya gabata ne jam'iyyar ta APC ta bayyana cewa Gwamnan ba zai Iya fitowa takara a karkashin jam'iyyar ba, saboda wasu 'yan matsaloli da aka lura da su a takardun makarantarsa..

Lamarin da gwamnan ya karyata bayan da ya fice daga jam'iyyar ta APC.

PDP dai ta ce, "duk da cewar gwamnan zai dawo jam'iyyarmu, hakan ba wai yana nufin zamu fifita Obaseki kan sauna masu neman takara ba."

Mutane da dama na ganin ficewar gwamnan na da nasaba ne da sabanin da Gwamnan ya ke ta samu da shugaban jam'iyyar Adams Oshiomhole.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG