Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EFCC Ta Kaddamar Da Manhajar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Wayar Salula


EFCC

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC, ta kaddamar da wata manhaja ta wayar salula, wacce za ta rika amfani da ita a wajen aikin yaki da ayukan cin hanci da rashawa a kasar.

Shugaban Hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa ya bayyana cewa hukumar za ta yi amfani da ci gaban duniya na zamani da wasu sababbin fasohohi don kawar da ayyukan almudahana a Najeriya

Al’umma za su iya mafani da da sabuwar fasahar da hukumar ta samar wajen tura rahoton duk wasu kararraki da korafe-korafe na ayyukan cin hanci da rashawa zuwa ga hukumar kai tsaye.

Manhajar wacce ake kira da 'Idon Mikiya' wato ‘’EAGLE EYE’’ a cewar hukumar, za ta saukaka hanyoyin gargajiya da ka saba kai rahoton ayyukan almundahana na mutane ko hukumomi da ake zargi da aikata laifufuka.

Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa (Facebook/EFCC)
Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa (Facebook/EFCC)

Abdulrasheed Bawa ya kuma kara da cewa an kirkiri manhajar ne ta hanyar da za ta samar da tsaro ga duk wanda ya shigar da karar ayyukan cin hanci da rashawa ga Hukumar.

sai dai ya ce wannan ci gaban da aka samu ba wai zai soke sauran hanyoyin da aka saba kai rahoton karraki ga hukumar ba.

Kazalika, Bawa ya kara da cewa hukumar EFCC za ta yi kwakkwaran bincike akan duk wani korafi da aka aika mata ta sabuwar manhajar don tabbatar da cewa ba’a yi amfani da damar ba wajen tura sakon karya ko nuna son rai.

Ya kuma kara da cewa za’a yi amfani da hukuncin doka ga duk wanda aka kama da laifin aikata hakan

XS
SM
MD
LG