Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EFCC Za Ta Binciki Fannin Kasuwanci Da Ake Yi Ta Teku


A cikin matakan da hukumar yaki da cin hanci EFCC, ta Najeriya ta dauka, bayan tarukan ranar yaki da cin hanci ta duniya, akwai maida hankali kan hadahadar Teku da ta hada da tashoshin Teku da kasuwancin jiragen ruwa.

Wannan ya biyo bayan yadda gwamnatin Najeriya ta rufe kan iyakokin kasar da komawa kusan kacokan shigo da kaya ta ruwa.

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hancin ta EFCC, Ibrahim Magu, a taron da aka yi a fadar Aso Rock ya ce, hukumar za ta karfafa aiki da ka'idojin kasuwancin Teku don daukar matakan yaki da zarmiya.

Shugaban hukumar hada-hadar kasuwanci ta jiragen ruwa, Hassan Bello da ya zama babban mai ruwa da tsaki a taron ya nuna maraba da wannan mataki, ya ce, hakan zai taimakawa Najeriya wajen cin gajiyar kudin shiga masu yawa waje da man fetur.

Gwamnatin Najeriya ta hanyar hukumar kwastam za ta karfafa tashoshin sauke hajar teku a tudu da a ka kafa a sassan da basa kan iyakar ruwa, don saukakawa 'yan kasuwa dawainiyar tafiya mai nisa don daukowa ko tura hajar su ketare.

Shugaba Buhari ya yi bayanin ne lokacin da ya ke bude tashar ta tudu a Kaduna, inda yanzu a ke maganar bude ta Funtua, Kano, Filato da Maiduguri.

Saurari cikakken rahoton Wakilin muryar Amurka a Abuja, Nasiru Adamu El-hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG