WASHINGTON, D.C —
Gwamnatin jahar Filato ta ce ta kammala dukkan shirye-shirye don maida dukkan wadanda suka kaurace wa mahallansu, su ke kuma gudun hijira a wasu wurare, zuwa yankunansu na asali.
Komishinan ayyuka na musamman a jahar Filato, Irmiya Werr ya ce gwamnan jahar Simon Lalong, ya bada umurnin maida ‘yan gudun hijirar.
Shugaban karamar hukumar Barikin Ladi, Barista Ezekiel Mandyau, ya ce sun yi zaman tattaunawa da masu ruwa da tsaki, sun kuma amince kowa ya koma gidansa.
Shi kuma shugaban karamar hukumar Riyom, Mafeng Gwalson, ya bada tabbacin cewa gwamnati ta sanya matakan tsaro a yankunan domin ganin kowa ya zauna lafiya.
Wasu ‘yan gudun hjirar, sun yi na’am da matakan mayar da su garuruwansu.
A saurari rahoto cikin sauti.
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 20, 2023
Gwamnonin Gombe, Bauchi Sun Samu Wa'adi Na Biyu
-
Maris 19, 2023
Seyi Makinde Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Oyo
-
Maris 19, 2023
Yadda Aka Yi Zaben Gwamna A Bauchi
Facebook Forum