Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

El Zakzaky Na Shirin Neman Magani A Wata Kasa Baicin India


Sheik El-Zakzaky

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa shugaban 'yan Shia na IMN Ibrahim Elzazzaky ya so zullewa ne ta amfani da damar da kotu ta ba shi ta neman magani a Indiya.

Wannan labari ya fito ne wuni daya gabanin labarin cewa Elzakzaky ya kamo hanyar dawowa Najeriya don rashin gamsuwa ga yadda a ke shirin yi ma sa magani a asibitin Medenta na New Delhi a Indiya.

A sakon faifan bidiyo bayan na sauti, Elzakzaky ya ce sai a zabi mai gaskiya tsakanin sa da gwamnatin Najeriya.

A sanarwa daga babban sakatariyar ma'aikatar labaru Grace Isu Gekpe ta ce tun isar jirgin daular larabawa, Elzakzaky ya nemi amshe Fasfo din sa inda kuma bayan isa Indiya ya so sauka a babban hotel da kuma samun damar ganawa da jama'ar da ya ga dama.

Hana Elzazzaky samun wannan bukata ya sanya shi kin wani likita ya duba shi da kuma fitar da sakon sauti na nuna ya na cikin mafi munin hali.

Gwamnatin ta ce Indiya ta hana Elzazzaky amfani da kasar ta wajen fadada harkar kungiyar sa ta IMN zuwa ta duniya.

Sakon bai kammala ba sai da ya ba da hakuri ga gwamnatin Indiya don yadda Elzakzaky ya so bijirewa doka.

In za a tuna kakakin IMN Ibrahim Musa ya ce an sulhunta lamarin kuma jagoran na su zai karbi magani a Indiya bayan ganawa da likitocin da ya amince da su.

Me kungiyar IMN za ta ce ne yanzu kan dawowar Mallam Elzakzaky Najeriya?

Babban almajirin Elzazzaky, Muhammad Ibrahim Gamawa ya ce za su nemi tafiya wata kasar cikin zabin Malasiya,Indunsiya ko Turkiyya.

An ga wani hoto inda Elzazzaky ke ganawa da ministan kabilu marar sa rinjaye na Indiya Mukhtar Naqvi.

Ga dai rahoton da wakilin mu Nasiru Adam El Hikaya ya hada mana a kan batun:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG