Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

El-ZAKZAKY: An gudanar da zanga zanga a Illela


Sheikh Ibrahim Yaqub El-Zakzaky

Magoya bayan shugaban mabiya Shi’a a Najeriya Sheikh Ibrahim Yaqub El-Zakzaky sun gudanar da zanga zangar lumana a karamar hukumar Illela jihar Sokoto.

Masu zanga zangar sun shafe sama da sa’oi biyu suna zagaye na lumana, domin bayyana alhininsu bisa sumamen da jami’an soja suka kai gidan na shugabansu dake garin Zaria ranar asabar.

Sun bayyana cewa, sheri ne daga waje aka yiwa shugaban da ya sa aka kai sumamen. Bisa ga cewar kakakin masu zanga zangar, Sheikh El-Zakzaky yana daya daga cikin wadanda suke taimakawa wajen ci gaban Najeriya tsintsiya madaukinki daya.

Bisa ga cewar kakakin masu zanga zangar, Sheikh El-Zakzaky ne kadai wanda Allah ya ba basirar gane sherin kasashen waje dake neman ganin Najeriya ta wargaje, yana kuma yin tsayin daka wajen fadakar da magoya bayanshi game da irin wadannan sherin.

Sun kuma yi kira ga gwamnati ta saki shugabansu domin samun zaman lafiya.

Ga rahoton da wakilin Sashen Hausa Harouna Mamman Bako daga jamhuriyar Nijar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG