Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

#EndSARS: Batutuwa 15 a Jawabin Shugaba Buhari


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

'Yan Najeriya da kuma masu kula da lamura na kasashen ketare na ci gaba da tsokaci kan jawabin da shugaban Najeriya Muhamadu Buhari ya gabatar bayan zanga zangar neman kawo karshen cin zarafin al'umma da 'yan sanda ke yi.

Ga batutuwa sha biyar daga cikin ishirin da bakwai da shugaba Muhamadu Buhari ya tabo a jawabin nasa.

1.Ya zama dole a gare ni in yi magana da ku bayan na ji daga yawancin 'yan Najeriya da suka damu, sannan na kammala taro tare da dukkan shugabannin tsaro.

2. Dole ne in gargadi wadanda suka karkatar da akalar zanga zangar farko, sahihiya mai kyakkyawar niyya da wasu matasanmu su ka gudanar a sassan kasar nan, kan wuce gona da iri da wasu jami’an 'yan sanda masu yaki da fashi da makami da aka fi sani da SARS suka yi.

3. A ranar Litinin 12 ga watan Oktoba, na amince da hakikanin damuwa da koken jama'a su ka nuna game da yadda jami’an SARS ke amfani da karfi fiye da kima wajen aiwatar da ayyukan su.

4. Zabin yin zanga-zanga cikin lumana yancin ne ga ‘yan kasa kamar yadda sashi na 40 na kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar da sauran dokoki; amma wannan 'yancin yin zanga-zangar ya kuma aza wa masu zanga-zangar nauyin girmama hakkin sauran' yan kasar bisa tsarin dokar kasa.

5. A matsayina na Shugaba a tsarin mulkin damokiradiyya, mun saurara tare da yin la’akari sosai da bukatu guda biyar na masu zanga-zangar. Kuma muka amince da bukatun, nan da nan muka soke SARS sannan muka sanya matakai don magance sauran bukatun matasan.

6. Akan amincewa da dakatar da SARS, tuni na bayyana karara cewa hakan yayi daidai da kudurin mu na aiwatar da sauye-sauye a kan tsarin aikin ‘Yan Sanda.

7. Abin takaici, amsa bukatun na su cikin lokaci ya zama alama kamar gazawa kuma wasu sun karkatar da zanga-zangar saboda son zuciya da rashin kishin kasa.

8. Sakamakon wannan a bayyane yake ga duk masu lura: rayukan mutane sun salwanta; an bayar da rahoton ayyukan lalata da yara; an kaiwa manyan gidajen gyara hali guda biyu hari kuma aka saki masu laifi; an lalata kadarorin jama'a da dama; an keta fadar mai girma oba na Legas. Wadanda ake kira masu zanga-zanga sun mamaye filin Jirgin Sama na kasa da kasa a cikin hakan sun tarwatsa tsarin tafiye-tafiye na cikin gida da baki.

9. Duk wadannan aika-aika da sunan zanga-zangar END SARS. Gaskiya na yi matukar bakin cikin yadda aka rasa rayukan mutanen da ba su ji ba su gani ba kuma ba yadda za’a alakanta zanga-zangar lumana da irin dabi’un lalata dukiyoyi da aka yi.

10. Yadda aka yi ta yada karya ta hanyar kafafen sada zumunta, musamman, cewa wannan gwamnatin bata kula da radadi da mawuyacin halin da ‘yan kasar ke ciki ba, wata dabara ce na tunzura mutane a cikin gida da wajen Najeriya.

11.Ayyukanmu da maganganunmu sun nuna yadda wannan gwamnatin ta himmatu ga jin daɗin 'yan ƙasa duk da matsin tattalin arziki da kasar ke ciki, da ƙarin nauyi da ƙuntatawa sakamakon bullar cutar ta Coronavirus.

12. Gwamnati ta tanadi tsare-tsare na musamman ga matasa, mata da kuma marasa karfi a cikin al'ummar mu. Wadanda suka hada da babban shirinmu na fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci cikin shekaru 10 masu zuwa; kirkiro da Asusun Noma na Matasa, Asusun Matasa na Biliyon 75 don samar da dama ga matasa da Kananan da Matsakaitan Masana'antu (MSME) Asusun Rayuwa wato survival fund, da gwamnati ta tanada.

13. Babu Gwamnatin Nijeriya da ta gabata da ta fitar da irin wannan hanyoyin magance talauci kamar yadda muka yi.

14. Dangane da walwalar ‘yan sanda, an umarci hukumar kula da albashi ta kasa, da ta hanzarta aiki kan kammala sabon tsarin albashi na‘ yan sandan Najeriya. Hakanan ana sake duba abubuwan da ke cikin sauran ayyukan tsaro.

15. Wannan gwamnatin tana mutuntawa kuma za ta ci gaba da mutunta duk haƙƙoƙin dimokiraɗiyya da 'yanci jama'a, amma ba za ta ƙyale kowa ko ƙungiyoyi su tarwatsa zaman lafiyar al'ummarmu ba.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG