Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

#EndSARS:'Yan Sanda Sun Zubawa Matashi Fetir A Baya Suka Cinna Mashi Wuta a Binuwe


Zaman sauraron kararrakin wadanda rundunar SARS ta ci zarafin su.

Wadanda jami'an rundunar 'yan sandan SARS suka ci zarafin sun fara bada bahasi gaban kwamitin bincike da aka kafa a fadin Najeriya biyo bayan zanga zangar da matasa suka yi da nufin yi wa rundunar iyaka.

Sama da wata guda bayan zanga zangar lumana da matasa a birane da dama na Najeriya suka gudanar na neman soke sashen rundunar ‘yan sanda da ke yaki da masu aikata miyagun laifuka, da suka hada da fashi da makami, da ake kira SARS a takaice, wannan gangamin mai taken #EndSARS yana ci gaba da zama kan gaba a cikin batutuwan da ke daukar hankali a Najeriya da kuma kasashen waje.

Sai dai rushe wannan rundunar da gwamnatin tarayya ta yi bai gamsar da masu zanga zangar ba, wadanda suka bukaci a hukumta jami’an tsaron da aka tabbatar sun gasawa jama’a akuba, yayinda suke kuma bayyana rashin amincewa da kafa sabuwar runduna da suna SWAT da zata maye SARS. Bisa ga cewar masu zanga zangar, rundunin biyu Danjuma ne da Dan jummai, babu abinda ya sauya sai dai suna.

Wani yana bada bahasi gaban kwamitin da ke zama a kotun tarayya Maitama, Abuja
Wani yana bada bahasi gaban kwamitin da ke zama a kotun tarayya Maitama, Abuja

Wani wanda ya bayyana gaban kwamitin dake zama a jihar Binuwe ya bada labari mai sosa rai na irin akubar da jami’an SARS suka gasa masa.

Yace, "Sun rika kwama min kulki a guiwoyin da kuma kwauri na. Bayan haka suka kwara min man fetir a baya, daga nan suka yi amfani da abin kunna taba suka cinna min wuta. Da na ji azaba ta ishe ni sai na amsa laifin da ban aikata ba domin in rage shan azaba, ban sani ba ashe na kara sa kaina cikin wata sabuwar masifa."

Sai dai ko baya ga rundunar tsaro ta SARS akwai wadansu sassan rundunar ‘yan sanda da suke gudanar da ayyuka makamantan na SARS da ake bayyana cewa wadansu lokuta jami’an wadannan sassan ne suke cin zarafin al’umma amma a dora alhakin kan rundunar SARS.


Sauran bangarorin aikin ‘yan sandan sun hada da:Police Mobile Force PMF masu kwantar tarzoma, Rapid Response Squads RRS-‘masu bada agajin gaggawa, Intelligence Response Team IRT- masu tattara bayanan sirri, Special Tactical Squad STS-masu gudanar dacayyuka na musamman, Special Anti-Kidnapping SAKU-masu ceto wadanda aka yi garkuwa da su, Special Protection Unit SPU-Masu bada kariya ta musamma,Special Weapons And Tactics SWAT-mai dakile laifukan da ake amfani da makamai, rundunar da ta maye gurbin SARS.

Wani jami'i da wani mutum ya ambata a jerin wadanda suka keta hakin sa
Wani jami'i da wani mutum ya ambata a jerin wadanda suka keta hakin sa

DCP Frank Mba kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya ya bayyana cewa, rundunar ‘yan sanda tana da bangarori da dama kuma wadansu lokuta ayyukansu suna da alaka da juna.

Wadannan rundunoni su ake kira “Tactical Squads,” banbancinsu da ‘yan sandan yau da kullum wato “conventional police” shine, su suna tunkarar manyan laifuka ne masu hatsarin gaske, kamar masu garkuwa da mutane ‘yan bindiga dadi, ‘yan fashi da makami, ‘yan ta'adda irin su Boko Haram da dai sauran manyan laifuka, na biyu kuma, ‘yan sandan yau da kullum wato “Conventional police” suna aiki ne a Caji Office, suna kuma tunkarar kanana da matsakaitan laifuka kamar rigimar miji da mata, rigimar bashi. rigima tsakanin makwabta da makamantansu.

ana-zargin-wani-dpo-da-azabtar-da-mutane-da-tabarya-a-bauchi

filato-ta-fara-karbar-korafe-korafen-cin-zarafin-jama-a-da-ake-zargin-jami-an-tsaro-sun-yi

endsars-sojoji-sun-bada-bahasi-gaban-kwamitin-bincike

Wannan rundunar tana da rasirin ainun kasancewa duk masu aikata miyagun laifuka suna kaffa kaffa da shiga hanunsu, sannan horon ‘yan sandan yau da kullum ba za su iya tunkarar manyan laifuka kamar yan bindiga ko yan ta'adda ba. Amma wadannan suna aiki kamar kannen sojoji ne.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya bayyana cewa, sabuwar rundunar SWAT ba ta da alaka da rundunar da ta gabace ta.

Galibin 'yan Najeriya da Muryar Amurka ta yi hira da su sun bayyana cewa basu san akwai banbanci tsakanin jami'an 'yan sandan ba, basu kuma san yadda aikinsu ya banbanta ba. Yayinda suka abinda abinda jami'an SARS suke yi baya cikin tsarin aikin 'yan sanda.

Rundunar ‘yan sanda mai yaki da fashi da makami dai ta yi kaurin suna ne sabili da yadda take amfani da karfin “soji” yayin gudanar da aikinta inda mutane da dama suka rika bayyana cewa ta zama tamkar kungiyar ‘yan banga da take tada hankalin al’umma a duk inda ta shiga.

Daga cikin wadanda suka dandana kudarsu a hannun ‘yan sandan, akwai gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi wanda ya bayyana irin yadda ‘yan sanda suka gasa mashi aya a hannu a shekara ta dubu biyu da goma sha hudu. Da yake jawabi a wani taron tuntuba da samun masala dangane da batun #EndSARS da aka gudanar a jihar Ekiti, gwamnan yace zanga zangar #EndSARS dama ce ta yiwa aikin ‘yan sanda baki daya garambawul.

Zaman sauraron kararrakin wadanda rundunar SARS ta ci zarafin su
Zaman sauraron kararrakin wadanda rundunar SARS ta ci zarafin su

A cikin wani jawabi da ya yi a wani bukin yaye daliban makaranta, Basaraken gargadiya na Ife, Ooni Iffe, Oba Adeyeye Ogunwusi ya bayyana cewa, matasa suna shiga zanga zanga da tada zaune tsaye ne domin rashin samun biyan bukata. Basaraken ya bayyana cewa, tilas ne ‘yan siyasa da shugabannin al’umma su maida hankali wajen inganta rayuwar matasa saboda idan ba a inganta rayuwar matasa suka iya dogaro ga kansu ba, zanga zangar da suka yi wasan yara ce idan aka kwatanta da abinda za su iya yi nan gaba, Ya ce wauta ce a boye kudi a banki a bar mabukata suna fama da talauci.

Bincike na nuni da cewa, tsawon shekarun aikin rundunar SARS, jami’anta sun rika cin karensu ba babbaka yayinda suke cin zarafin jama’a da shiga sharo ba shannu ta wajen watsi da ainihin aikin ‘yan sanda suna shiga hakin al’umma da suka hada da sa baki a abinda ya shafi ma’aurata ko saurayi da budurwa.

Jami’an SARS sun yi kaurin suna wajen yiwa wanda suka kama dukan fitar hankali ko kwace, har ma da kisa.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG