Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Erling Haaland Ya Tafi Jinya


Erling Haaland

Haaland ya ci wa Dortmund kwallaye 70 a wasanni 69 tun bayan da ya koma kungiyar daga Red Bull Salzburg a shekarar 2019.

Dan wasan Borussia Dortmand Erling Haaland zai yi jinyar wasu makonni bayan wani rauni da ya ji a saman cinyarsa, kocin kungiyar Marco Rose ya ce.

A kwanan nan dan wasan ya dawo daga jinya bayan fama da ya yi da matsalar ciwon jijiya, inda har ya zura kwallo biyu a karawar da Dortmund ta doke Mainz da ci 3-1.

Hakan ya ba Dortmund damar darewa kan teburin gasar ta Bundesliga da ake bugawa a Jamus a karshen makon da ya gabata.

Sai dai a ranar Asabar Haaland dan shekara 21 ya fuskanci sabon kalubale a karawar da suka yi da Armenia Bielefeld a ranar Asabar.

Dan asalin kasar Norway, Haaland bai samu damar bugawa kasarsa wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ba da kasar Turkiyya, Latvia da Montenegro saboda ba a iya tafiya sanadiyyar ciwon jijiyar.

Haaland ya ci wa Dortmund kwallaye 70 a wasanni 69 tun bayan da ya koma kungiyar daga Red Bull Salzburg a shekarar 2019.

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Wasanni

Mece ce makomar kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer?

Ole Gunnar Solskjaer
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00
Karin bayani akan Wasanni

Lionel Messi: PSG

A karon farko, Messi ya nuna sabuwar rigar wasan kwallonsa ta PSG
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG