Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lukaku Zai Murmure Nan Ba Da Jimawa Ba – Pastorello


Lukaku a hannun hagu
Lukaku a hannun hagu

An sauya shi da Kai Havertz bayan da ya gurde kwaurinsa a lokacin da  dan wasan Malmo Lasse Nielson ya kwade shi.

Dan wasan Chelsea Romelu Lukaku zai murmure daga jinyar da yake yi nan ba da jimawa ba, in ji mai kula da dan wasan Feredrico Pastorello.

A ranar Laraba Lukaku ya fice a karawar da suka yi da Malmo a gasar cin kofin nahiyar turai ta Champions League a rukunin H inda aka gan shi yana dingishi yayin da yake ficewar.

An sauya shi da Kai Havertz bayan da ya gurde kwaurinsa a lokacin da dan wasan Malmo Lasse Nielson ya kwade shi.

Da ma kuma tun gabanin wasan wanda Chelsea ta lallasa Mamlo da ci 4-0, kocin Chelsea Thomas Tuchel ya ce gajiya ta taruwa Lukaku.

Sai dai eja dinsa Pastorello ya ce yana da kwarin gwiwa Lukaku zai yi saurin murmurewa daga raunin da ya ji.

Wannan koma baya da dan wasan dan asalin kasar Belgium ya gamu da ita na zuwa ne yayin da tauraronsa ke haskawa bayan komen da ya yi zuwa kungiyar ta Blues bayan da ya baro Inter Milan.

Ya zura kwallaye hudu a wasanni 11 da ya bugawa kungiyar a wannan kakar wasanni.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG