Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ethiopia: An kashe akalla mutane 40 a yankin Oromo


'Yan kabilar Oromo suna juyayin wadanda dakarun gwamnatin Ethiopia suka kashe akan mallakar filayen kakanin kakaninsu

Wata kungiyar kare hakin bil Adam ta ce an kashe akalla mutane arba'in a yankin Oromo inda'yan asalin wurin ke kushwa shirin gwamnatin kasar na yin anfani da filayensu.

Wata kungiyar kare hakkin bil’adama, ta ce akalla mutane 140 aka kashe a jihar Oromo da ke kasar Habasha ko kuma Ethiopia, a lokacin da jami’an tsaro suka far ma wasu masu zanga zangar kin jinin gwamnati.

Wannan adadi dai ya haura wanda hukumomin kasar suka fitar.

A yau juma’a, Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta ce, mutane 140 aka kashe kana aka jikkata wasu da dama, a arangamar da kungiyar ta ce ita ce mafi muni da ta samu kasar tun bayan shekarar 2005 da aka yi rikicin zabe.

Wannan adadi da kungiyar ta Human Rights Watch ta fitar ya ninka har sau biyu adadin da aka fitar a watan da ya gabata.

A baya gwamnatin kasar ta ce mutane biyar ne kacal suka mutu.

Zanga zangar ta samo asali ne bayan da wasu suka nuna adawarsu kan wani shirin gwamnati na yin gine-gine a wasu gonaki da ke wajen Addis Ababa, babban birinin kasar.

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG