Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EU: Ta Haramta Anfanin Gona daga Najeriya Shiga Turai


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

A lokacin da Najeriya ke neman wasu hanyoyin samun kudin shiga saboda faduwar farashin man fetur sai gashi tarayyar turai ta haramta anfanin gona daga kasar shiga kasashenta.

Matakin haramta anfani gona daga Najeriya shiga Turai kai iya yiwa tattalin arzikin kasar illa na wani karamin lokaci.

Amma daga baya zai zama alheri ga manoman Najeriya saboda zasu koya su kuma bin ka'idojin duniya na adana anfanin gona ta hanyar yin anfani da magunan kwari da aka amince dasu a duniya.

Sanata Forster Ogolo ya yi magana kan matakin da tarayyar turai ta dauka akan hana kai kayan anfanin gona daga Najeriya.

Matakin ya biyo bayan gargadin da tarayyar Turai ya yiwa Najeriya har sau hamsin akan irin magunan kwari da bai kamata ta yi anfani dasu ba amma ta yi kunnen shegu.Najeriya ta shigaba da yin anfani da wani sinadarin kare lafiyar wake dake da illa. Manoma a Najeriya basu yi anfani da gargadin ba tun shekarar 2013.

Lokacin da aka kai maganar majalisar dattawa basu dauki wani kwakwaran mataki ba har maganar ta zama kalubale yau ga hukumomin noma da tanada abinci na Najeriya.

Yakamata a soma wayar da kawunan manoma saboda yadda ake tanada kayan noma da zasu kasuwannin ketare.

Tarayyar turai ta haramta kayan gona har guda arba'in daga Najeriya. Manoman Najeriya na anfani da wasu magunguna da idan an sasu cikin kayan gona za'a dauki kusan watanni shida kafin a iya cinsu idan ana son a gujwa hadari.

Majalisa zata dauki matakin warware matsalar. Najeriya ta kirkiro wata sabuwar hanyar tanada anfanin gona ba tare da yin anfani da magunguna masu guba ba.

Manoman Najeriya kan kai wake ko ridi ko koko kasuwar Turai don sayarwa.

Sai dai NAFDAC tace rashin bin ka'idojinta ne da manoman ke yi ya jawo masu wannan hasarar.

Grahoton Nasiru Adamu El-Hikaya

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00

XS
SM
MD
LG