Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Facebook Ya Sauya Sunansa Zuwa “Meta”


Shugaban Facebook CEO Mark Zuckerberg yayin da yake sanar dasabon sunan Facebook wanda ya koma "Meta", a ranar 28 ga watan Oct. 2021.
Shugaban Facebook CEO Mark Zuckerberg yayin da yake sanar dasabon sunan Facebook wanda ya koma "Meta", a ranar 28 ga watan Oct. 2021.

Wannan mataki na sauya sunan na zuwa ne yayin da kamfanin ke fuskantar wasu kalubalen da suka shafi zargin da ake masa na fifita riba akan kare masu amfani da shafin.

Shugaban Facebook Mark Zuckerberg ya ce kamfanin ya sauya sunansa zuwa “Meta,” yayin da yake daukan wasu matakai na kara rungumar wasu sabbin fasahohi don tafiya da zamani.

A ranar Alhamis Zuckerberg ya sanar da wannan sauyi.

Kamfanin ya ce yana so ya taka wani sabon matsayi inda masu amfani da shi za su rika kallon shafin a matsayin shafin sada zumunta mai kusurwa uku a maimakon biyu.

“Dandalin sadarwa na gaba da za mu fitar, zai zamanto abin burgewa, inda za ku rika ganin kanku a cikin abin da ke faruwa, ba kawai ku tsaya a matsayin ‘yan kallo ba.” Zuckerberg ya ce.

Sabuwar fasahar da kamfanin zai samar, zai sauya matsayin masu ziyartar shafin daga matsayi na 'yan kallon abin da ke faruwa zuwa matsayin da za su shiga har a dama da su a abin da ake yi.

Hakan zai samu ne ta hanyar amfani da fasahar nan ta shiga sararin duniyar yanar gizo ko kuma “Virtual Reality” a turance, inda mutum zai rika ganin kansa a cikin yanayin da yake kallo.

Wannan mataki na sauya sunan na zuwa ne yayin da kamfanin ke fuskantar wasu kalubalen da suka shafi zargin da ake masa na fifita riba akan kare masu amfani da shafin.

Bayanan sirri da wata tsohuwar ma’akaciyar kamfanin Frances Haugen ta kwarmata a kwanan nan, sun sa mahukunta sun fara yin nazari mai zurfi kan shafin.

Ana zargin kafar ta Facebook da ba da kofar cin zarafin bil adama, furta kalaman kiyayya, wajen watsa labaran boge da batutuwan da suka shafi haifar da rashin lafiyar kwakwalwa.

Kamfanin ya musanta duk wadannan zarge-zarge.

XS
SM
MD
LG