Accessibility links

Fada a arewacin Mali ya yi sanadin mutuwar mutane 20

  • Ibrahim Garba

Ag Intalla Algabass, wani shugaban Ansar Dine

Shaidu a arewacin Mali sun ce an kashe akalla mutane 20 a jiya Laraba a wata gwabzawar da aka yi

Shaidu a arewacin Mali sun ce an kashe akalla mutane 20 a jiya Laraba a wata gwabzawar da aka yi tsakanin ‘yan kishin Islama masu dauke da makami da ‘yan tawayen da ke gwagwarmayar kafa kasar Asbinawa zalla a yankin.

Wani wakilin Muryar Amurka y ace wannan kungiyar da ke da alaka da kungiyar al-Qaida mai suna MUJAO (Kungiyar Hada Kai Don Ayyukan Jihadi a Afirka ta Yamma) ta kwace muhimmin garin nan na Gao daga wajen kungiyar a ware ta MNLA (Kungiyar Kubutar da Azawad ta kasa) bayan mummunan musayar wuta a dukkan tsawon rana.

Ya ce ba a san tabbataccen adadin wadanda su ka mutu ba kuma wasu da dama sun sami raunuka, ciki har da fararen hula. Y ace bayan an fatattaki ‘yan awaren daga garin Gao, an cigaba da gudanar da harkokin rayuwa kamar yadda aka saba, ta yadda aka bude shaguna ‘yan kasuwa kuma su ka je harkokinsu a kasuwar.

Kungiyar ta MNLA da masu kishin Islama dauke da makami wato Ansar Dine sun kame arewacin Mali a farkon wannan shekarar. Dukkannin bangarorin biyu sun kunshi ‘yan kabilar Asbinawa daga zuru’o’i dabam-dabam.

To amman a sa’ilinda ita Kungiyar MNLA ke son a kafa ‘yantatattar kasar Asbinawa zalla mai suna Azawad a arewacin Mali, ‘yan kishin Islamar sun ce su so su ke daukacin kasar Mali ta kasance mai bin tafarkin Shari’ar Musulunci. Bangarorin biyu dai sun sha fafatawa cikin ‘yan makwannin nan.

A babban birnin kasar Bamako a jiya Laraba, ‘yan gudun hijira daga arewacin mali sun gudanar da zanga-zangar a rana ta biyu a daura da ofishin Firayim Minista su na kiran gwamnati ta dau mataki game da al’amarin na arewa.

XS
SM
MD
LG