Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fada Tsakanin Sojojin Sudan Ya Halaka Mutane 50


Soja daga rundunar mayakan sudan.

Rundunar sojojin Sudan tace fada ‘yar gida kan ballewar kudancin kasar ya kashe mutane 50.

Rundunar sojojin Sudan tace fada ‘yar gida kan ballewar kudancin kasar ya kashe mutane 50.

Gwabzawar baya bayan nan ya faru ne a garuruwa biyu dake can dan nesa da kogin Nilu. Jami’ai suka ce fadan ya barke ne a garuruwan Melut da Paloich ranar Asabar bayanda sojoi daga kudancin kasar suka ki bin umarnin su janye zuwa arewacin kasar.

Fadace fadacen ya fara ne ranar Alhamis tsakanin sojoji daga arewa da kumakudancin kasar a garin Malakal. Rundunar sojojin kasar tace fadan ya tashi ne bayanda sojoji daga kudancin kasar suka ki mika makamansu ga arewaci.

Ana sa ran sabuwar jamhuriyar Kudancin Sudan zata ayyana 'yanci cikin watan Yuli.

XS
SM
MD
LG