Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe mutane ashirin a kasar Sudan a wata arangamar sojoji


Sojojin kasar Sudan.

Jami’an sojin kasar Sudan sun ce an kashe mutane 20 a wani fadan da ya barke tsakanin sojojin kasar

Jami’an sojin kasar Sudan sun ce an kashe mutane ashirin a wani fadan da ya barke tsakanin sojoji sakamakon rashin amincewa da sake wurin aiki da wadansu sojojin suka yi, yayinda kudancin kasar ke shirin zama kasa mai cin gashin kai. Fadan ya kaure ne ranar alhamis a garin Malakal lokacin da wani bangaren rundunar sojin yaki mika manyan makamai da za a tura arewaci. A kalla mutane ashirin da hudu suka ji raunuka a fadan. An yi wannan fadan ne a daidai lokacin da kudancin kasar ke shirin cin gashin kai bayan kuri’ar raba gardaman da aka kada sakamakon yarjejeniyar da aka cimma cikin shekara ta dubu biyu da biyar ta kawo karshen yakin basasa tsakanin arewa da kudancin kasar.

XS
SM
MD
LG