Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fada Ya Sake Tilastawa 'Yan Sudan Ta Kudu Shiga Kasar Uganda


'Yan gudun hijira daga Sudan ta Kudu
'Yan gudun hijira daga Sudan ta Kudu

'Yan gudun hijarar Sudan Ta Kudu, wadanda suka ketare zuwa kasar Uganda mai makwabtaka da su, daga karamar hukumar Morobo ta jahar Yei River, sun ce mutane fa na mutuwa a sansanonin 'yan gudun hijira.

Sun gudu ne yayin da aka yi fada tsakanin sojojin gwamnati da wata kungiyar mayaka, kuma su na kira gwamnati da ta zauna da kungiyar don ta san bukatunta a kuma tattauna yadda za a cimma jituwa.

Fararen hula daga Karamar Hukumar ta Morobo sun ce babbar hanyar da ta hada Uganda da Sudan Ta Kudu, a yanzu ba a iya binta saboda yadda 'yan bindigar ke datse hanyar.

'Yan gudun hijira daga Sudan ta Kudu
'Yan gudun hijira daga Sudan ta Kudu

Akasarin masu gujewa daga yankin kan ratsa ta Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ne, kafin su isa Ugandar, tafiya mai tsawon kilomita 50.

Wani mazaunin Morobo mai suna Moro Moses, ya tsere daga yankin da matansa biyu da 'ya'yansa biyu da kafa a karshen makon jiya bayan da rikici ya sake tashi. Ya ce ya na fatan za a sake samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Sudan Ta Kudu don ya koma gida da iyalinsa.

Kwanaki biyu da su ka gabata, Luiza Dawa ya tsere daga Morobo ya ratsa ta Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo zuwa kasar Uganda, ya ce akasarin hanyoyin da ke Sudan Ta Kudu na shake da 'yan bindiga, ta yadda akwai matukar hadari ga farar hula.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG