Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadar Gwamnatin Amurka Ta Ce Ba Za Ta Ba Wa Majalisar Waklilan Kasar Hadin Kai Ba


Fadar Gwamnatin Amurka ta White House, ta ce ba za ta shiga cikin abin da ta kira bincikin yiwuwar tsige Shugaba Trump ba, domin ba shi da hurumi a dokar kasar.

Lauyan fadar gwamnatin, Pat Cipollone, ya aikawa shugabannin ‘yan Democrat na majalisar wakilai wata wasika mai shafi takwas, ciki har da shugabar majalisar Nancy Pelosi, wadanda ke bincike kan ko Shugaba Trump ya karya doka ko akasin haka, da ya nemi Ukraine ta binciki Joe Biden da ke neman tikin takarar shugaba kasa karkashin jam’iyyar Democrat.

A cewar Lauyan, ‘yan Democrat sun karya dokar da ke tabbatar da “yin adalci da kuma matakan bin doka sau da kafa.”

Shugaba Trump dai ya sha musanta aikata ba daidai ba, inda har ya kan caccakin ‘yan Democrat saboda wannan bincike da suka sa a gaba.

Fadar gwamnmatin ta White House dai, ta yi kira ga shugabar majalisar wakilan Nancy Pelosi, da ta kira a kada kuri’a kan binciken tsige shugaban a daukan majalisar, idan kwamitocin da ke jagorantar binciken na so jami’an gwamnmatin Trump su ba da hadin kai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG