Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadar Shugaban Amurka Ta Yi Fushi da Alkalin da Ya Yi Watsi da Umurnin Hana 'Yan Wasu Kasashe Shiga Amurka


Donald Trump, shugaban Amurka

A cikin fushi Fadar White House ta mayar da martani wa alkalin da ya haramta yin aikin da dokar Shugaba Trump ta hana al'ummar wasu kasashe shiga Amurka

Fadar shugaban Amurka ta White House ta maida martani cikin fushi ga wani alkalin kotun tarayya da ya dakatar da sabon umurnin shugaba Trump, na haramtawa wasu kasashe shiga kasar, umurnin da ya kamata a ce ya fara aiki da safiyar yau Laraba.

“Wannan hukunci mai cike da hadari da kotun Gundumar ta yanke, ya dakile yunkurin da shugaba Trump ke yi na tabbabatar da tsaron Amurkawa, da kuma daukan matakan tsaro mafiya kankanta na hana shiga Amurka.” Wata sanarwar Fadar ta White House ta ce, jim kadan bayan da alkali Derrick Watson ya yi watsi da umurin da gwamantin Trump ta bayar na hana wasu matafiya daga kasashe shida shiga Amurka, saboda sun gaza ba da wasu gamsassun bayanai da za su yi daidai da matakan tsaron Amurka.

A nata bangaren, ma’aikatar shari’ar Amurka ta kwatanta matakin kotun a matsayin kuskure, tana mai cewa za su daukaka kara cikin gaggawa.

Da ba dan wannan hukuncin kotun ba, da umurnin na shugaba Trump ya haramtawa matafiya daga kasashen Chadi da Libya da Iran da Somalia da Syria da kuma Yamal shiga Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG